![]() |
| Abdullahi Shehu |
Lalatattun shugabanni, bare gurbin malamai tare da 'Yan boko akida sun dade suna gasa mana gyada a hannu.
- LALATATTUN SHUGABANNI sune suke rike da madafun iko a kasar nan shekara da shekaru ba tare da sun tsinanama kasar nan komai ba face kwashe dukiyar kasa da kuma jefa kasar cikin mawuyacin hali irin Wanda muke ciki a yau.
Su irin wadannan shugabanni basu amfanar kowa da komai face iyalansu da 'Yan 'uwan matansu, sai kuma mutane kalilan da suka san za suyi masu amfani wajen biyan bukatunsu na sharri.
- BARE GURBIN MALAMAI kuma sune irin malamai da wadancan shugabanni ke amfani dasu wajen biyan bukatarsu ta hanyar basu kudade don tara masu jama'a suyi masu addu'o'i kodai anan gida Najeriya kokuma a kasa mai tsarki Saudiyya.
- YAN BOKO AKIDA sune wadanda babu ruwansu da duk wata harka data shafi addininsu, da addini ya sami cigaba da karya samu babu ruwansu madamar zasu cigaba da kasancewa a office dinda yake. Hasalima idan kayi masu magana akan addini zasuce maka suba yan tsatstsauran ra'ayi bane bakuma addini ya kawo sua wannan matsayi ba.
Zamu cigaba Inn shaa Allah!

6 comments:
Allah dai ya kyauta.
Hmmm
Hmmm, speechless
Hmmm, speechless
Hmmm, speechless
Speachless too @ hussein
Post a Comment