A duk lokuttan da zaka zagaya
makarantunmu, za kayi kacibus da matsaloli iri daban daban. Wadanda suka hada
da rashin isassun Malamai, qarancin ababen zama da rubutu, sanyi-sanyi wajen
gudanar da aiki daga 6angaren Malamai; da dai sauran matsaloli nan-da-can.
Da dama, mu kanyi tunani da tambayar
‘menene ummul-aba’isin’ wadannan matsaloli da Ilimin yake samu. A wannan
kasida, munyi duba izuwa Kungiyar Malamai ta NU..T da Rashawa akan manya-manyan
matsalolin da suke addabar huddatayyar Ilimi a Jihar Katsina.
Kungiyar N.U.T kamar yadda kowa ya
sani, Kungiya ce wadda aka assasa ta don kare haqqin Malamai da Malumta a fadin
Kasar Najeriya. Duk da cewar ta wani fannin suna dan yin qoqari; amma mafi
yawanci tagomashin da Ilimi yake samu ya samo asali ne da irin yadda ake
tafiyar da ita wannan Kungiya.
Zamu iya cewa, abinda Kungiyar N.U.T
tafi qwarewa akan shi shine YAJIN AIKI (Strike); wanda koda sunyi shi ma ba
wani da mai ido yake haifarwa ba. Sauran Kungiyoyi, alal misali na ma’aikatan
lafiya; sunyi rawar gani a Jiha ta wajen kawo cigaba da walwala (welfare) ga
‘ya’yan su – kama daga Karin albashi, Karin girma, kudaden alawus-alawus da
sauransu.
Amma abin takaici ga 6angaren Malamai
shine, yadda ita wannan Kungiya take tatsar su (task) a kowane wata ba tare da
kwalliya na biyan kudin sabulu ba. Kuma a aikace ba wani aikin da za’a iya nuna
maka ace yau gashi N.U.T tayi shi.
A Jihar Katsina, irin salon Mulkin da
N.U.T ke gudanarwa yana daya daga cikin abubuwan dake kawo cikas ga cigaban
ilimi birni da kauye; kuma idan ba mataki aka dauka ba, to wannan matsalar zata
ci gaba da kasancewa kenan har ranar da ba’a sani ba.
SIYASA
Wannan ma wata babbar matsala ce wadda
take addabar cigaban Ilimi a Jihar Katsina, ta yadda ‘yan siyasa suke da
fada-a-ji musamman idan aka zo daukar ma’aikata, inda zaka ga sai dan
wane-da-wane ne kadai ke samun shiga. Ko kuma, wanene ka sani, ko wanene ya
aiko ka? Wannan kuwa ya jaza daukar Malamai wadanda basu da qwarewa kuma basu
san makamar aiki ba.
Idan har Gwamnati da ‘yan siyasa zasu
dauke hannunsu ga maganar daukar ma’aikata, a barwa hukumomin da abin ya shafa;
to na tabbatar za’a samu cigaba mafi inganci domin kuwa sai wanda ya cancanta
ne kawai za’a baiwa dama.
Akwai makarantu da dama wadanda idan ka
bincika zaka ga cewa akwai Malamai maza da mata wadanda basu zuwa wajen aiki,
wasu koda sunzo to basu gudanar da aikin su, wasu kuwa idan har zaka ga yadda
suke koyarwa to zaka iya zubar da hawaye domin tunanin yadda makomar ‘ya’yanmu
da qannenmu zata kasance. Kuma baka iya cewa KANZIL saboda su irin wadannan
Malamai Matan wasu ne, ko ‘ya’yan wasu, ko dangin wasu.
RASHAWA
Muhimmin abinda ya kashe Kungiyar N.U.T
da Siyasar kasar mu shine Rashawa – Rashawa kuwa kowa yasan tana cin ayyuka ne
kamar yadda iska ke tafiyar da ruwa.
A yanzu, zaka ga cewa idan mutum zai
kai ‘ya’yanshi makaranta sai ya hada da bada cin hanci da rashawa domin a dauke
su. Musamman idan yasan basu kai matakin daya kamata a dauke su din ba. Malamai
a makaranta sun maida rashawa kamar ruwan sha, ta yadda zaka ga Malami/Malama
suna fifita ‘ya’yan masu kudi ko sarauta fiye da ‘ya’yan talakkawa.
Ko wajen transfer ta Malamai zuwa wasu
makarantu, hukumomi suna taka rawa wajen barbadawa rashawa taki, a inda zaka ga
matar wane da wane ko ‘dan wane da wance an ajiye su acikin gari, su kuwa
malamai marasa galihu an watsa su kauyuka sannan an bisu da binbinin dubiya
(supervision).
Idan har bamu taru muka yiwa wannan
tufkar hanci ba, to lalle zamuci gaba da kasancewa cikin bango-daya (square
one) ba tare da mun samu cigaban daya kamata ba.
***** ****** *******
Muna buqatar muji ra’ayoyinku akan hanyoyin
magance wadannan matsaloli.
Sharhi,
Yusuf Umar Dutsin-ma
08031178528

No comments:
Post a Comment